1 Corinthians 4

Manzannin Kiristi

1Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah. 2Yanzu fa, ana bukatar waɗanda aka ba su riƙon amana, dole su zama masu aminci. 3Ƙaramin abu ne a gare ni a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a wata kotun mutane, ai, ko ni kaina ba na yanka wa kaina hukunci. 4Lamirina bai ba ni laifi ba, sai dai wannan bai mai da ni marar laifi ba. Ubangiji ne mai hukunta ni. 5Saboda haka, kada ku shariʼanta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

6To, fa ʼyanʼuwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba. 7Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?

8Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna-kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku! 9Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin ƙallo ga dukan duniya, ga malaʼiku da kuma mutane. 10Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu! 11Har yǎ zuwa wannan saʼa, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. 12Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka laʼanta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; 13in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yǎ zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

14Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ʼyaʼyana ne, ƙaunatattu. 15Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara. 16Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni. 17Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a koʼina, a kowace ikkilisiya.

18Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagan kai. 19Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Saʼan nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko. 20Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko. 21Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai?

Copyright information for HauSRK